John 10

Makiyayi da Garkensa.

1“Gaskiya nake gaya muku, mutumin da bai shiga wurin kwanan garken tumaki ta ƙofa ba, amma ya hau ta wata hanya dabam, ɓarawo ne ɗan fashi kuma. 2Mutumin da ya shiga ta ƙofa makiyayin tumakinsa ne. 3Mai gadin yakan buɗe masa ƙofa, tumakin kuma sukan saurari muryarsa. Yakan kira tumakinsa da suna yǎ kuma fid da su waje. 4Saʼad da ya fitar da dukan nasa a waje, sai ya ja gabansu, tumakinsa kuma sukan bi shi domin sun san muryarsa. 5Amma ba za su taɓa bin baƙo ba; sai dai su guje shi domin ba su san muryar baƙo ba.” 6Yesu ya yi wannan karin maganar, amma ba su fahimci abin da yake faɗa musu ba.

7Saboda haka Yesu ya sāke cewa, “Gaskiya nake gaya muku, ni ne ƙofar tumakin. 8Duk waɗanda suka riga ni zuwa ɓarayi ne, ʼyan fashi kuma, amma tumakin ba su saurare su ba. 9Ni ne ƙofar; duk wanda ya shiga ta wurina zai sami ceto. Zai riƙa shiga yǎ fita yǎ kuwa sami wurin kiwo. 10Ɓarawo yakan zo don yǎ yi sata ne kawai da kisa da kuma ɓarna. Ni kuwa na zo ne don su sami rai, su kuma same shi a yalwace.

11“Ni ne makiyayi mai kyau. Makiyayi mai kyau yakan ba da ransa domin tumakin. 12Wanda aka ɗauko haya ba shi ne makiyayi mai tumakin ba. Saboda haka saʼad da ya ga kyarkeci yana zuwa, sai yǎ sheƙa da gudu yǎ bar tumakin. Sai kyarkecin yǎ kai wa garken hari, yǎ kuma watsar da su. 13Mutumin yakan gudu don shi ɗan haya ne kawai, bai kuwa damu da tumakin ba.

14“Ni ne makiyayi mai kyau; na san tumakina, tumakina kuma sun san ni—  15kamar yadda Uba ya san ni, ni kuma na san Uba-ina kuwa ba da raina domin tumakin. 16Ina kuma da waɗansu tumakin da ba na wannan garken ba ne. Dole ne in kawo su. Su ma za su saurari muryata, za su kasance garke guda ɗaya da kuma makiyayi guda. 17Abin da ya sa Ubana yake ƙaunata shi ne, domin ina ba da raina-in kuma ɗauko shi. 18Ba mai ƙwace mini shi, sai dai don kaina nake ba da shi. Ina da iko in ba da shi, ina da iko in ɗauko shi kuma. Wannan umarni kuwa daga wurin Ubana ne na karɓo.”

19Saboda waɗannan kalmomi fa, Yahudawa suka sāke samun baraka a cikinsu. 20Da yawa daga cikinsu suka ce, “Yana da aljani yana kuma hauka. Don me za ku saurare shi?”

21Amma waɗansu suka ce, “Kai, waɗannan kalmomi ba na mai aljani ba ne. Aljani yana iya buɗe idanun makaho?”

Rashin Bangaskiyar Yahudawa

22Sai lokacin Bikin Miƙawa
Wato, Hanukka
a Urushalima ya kewayo. Lokacin sanyin hunturu ne,
23Yesu kuwa yana a filin haikali yana zagawa a Shirayin Solomon. 24Yahudawa suka taru kewaye da shi, suna cewa, “Har yaushe za ka bar mu cikin shakka? In kai ne Kiristi ka faɗa mana a fili mana.”

25Yesu ya amsa, ya ce, “Na faɗa muku, amma ba ku gaskata ba. Ayyukan banmamakin da nake yi cikin sunan Ubana suna shaida ni, 26amma ba ku gaskata ba domin ku ba tumakina ba ne. 27Tumakina sukan saurari muryata; na sansu, suna kuma bi na. 28Ina ba su rai madawwami, ba za su taɓa hallaka ba; ba kuma mai ƙwace su daga hannuna. 29Ubana, wanda ya ba ni su, ya fi duka girma, ba mai ƙwace su daga hannun Ubana. 30Da ni da Uba ɗaya ne.”

31Sai Yahudawa suka sāke ɗebo duwatsu don su jajjefe shi, 32amma Yesu ya ce musu, “Na nuna muku manyan ayyukan banmamaki daga wurin Uba. A kan wanne a cikinsu kuke so ku jajjefe ni?” 33Sai Yahudawa suka ce, “Ba don wani daga cikin waɗannan muke so mu jajjefe ka ba, sai don saɓo, kai da kake mutum kawai, kana mai da kanka Allah.” 34Yesu ya amsa musu ya ce, “Ba a rubuce yake a cikin Dokarku ba cewa, ‘Na ce ku alloli ne’
Zab 82.6
?
35In har ya kira su ‘alloli’, waɗanda maganar Allah ta zo musu-Nassi ba zai karyuwa ba—  36me za ku ce game da wanda Allah ya keɓe wa kansa ya kuma aiko duniya? Don me kuke zargi na a kan saɓo, don na ce, ‘Ni Ɗan Allah ne?’ 37Kada ku gaskata da ni in ba abin da Ubana yake yi ne nake yi ba. 38Amma in ina yinsu, ko ba ku gaskata da ni ba, ku gaskata da ayyukan banmamakin, don ku sani ku kuma gane cewa, Uba yana a cikina, ni kuma ina a cikin Uba.” 39Sai suka sāke yin ƙoƙarin su kama shi, amma ya kuɓuce musu.

40Saʼan nan Yesu ya sāke koma ƙetaren Urdun inda dā Yohanna yake baftisma. A can ya zauna 41mutane da yawa suka zo wurinsa. Suka ce, “Ko da yake Yohanna bai yi waata abin banmamaki ba, duk abubuwan da Yohanna ya faɗa game da mutumin nan gaskiya ne.” 42A nan kuwa mutane da yawa suka gaskata da Yesu.

Copyright information for HauSRK